Isa ga babban shafi

Sojoji dauke da makamai sun fitar da Moussa Dadis Camara daga gidan yarin Conakry

Wata majiyar shari'a ta kasar Guinea ta bayyana cewa, da safiyar yau Asabar ne wasu kwamandojin dauke da manyan makamai suka fitar da tsohon shugaban mulkin kama-karya na kasar Guinea Moussa Dadis Camara daga gidan yari, bayan wata mummunar musayar wuta da aka yi a tsakiyar birnin Conakry.

Moussa Dadis Camara, Tsohon Shugaban kasar Guinea
Moussa Dadis Camara, Tsohon Shugaban kasar Guinea © wikimedia.org
Talla

Harin na kwamandojin ya saka jama’ar birnin Conakry cikin zulumi kafin wayewar gari ga karar makamai masu sarrafa kansu.

An bayyana cewa wasu tsoffin jami’ai biyu da ake yiwa shari’a a halin yanzu da suka hada da Kyaftin Camara kan kisan kiyashin da aka yi a shekarar 2009 a karkashin shugabancinsa, na daga cikin mutanen da aka dauke daga gidan yari, a cewar wadannan majiyoyin, ba tare da bayyana ko Moussa Dadis Camara ya tsere da son ransa ba.

Zanga-zangar da sojoji suka murkushe a shekarar ta 2019
Zanga-zangar da sojoji suka murkushe a shekarar ta 2019 © AFP/Seyllou

Wata majiyar shari'a bisa sharadin sakaya sunanta ta ce, wasu sojoji da suka rufe fuskokinsu dauke da muggan makamai sun isa kofar gidan yarin da misalin karfe 4:00 na safe.

Sun bayyana cewa "sun zo ne domin su sako Kyaftin Dadis Camara", a cewar majiyar.

Majiyar ta karasa da cewa, maharan wadanda da alamun sun san wurin, sun nufi dakin da kyaftin din yake, inda suka tafi da shi da sauran wadanda ake tsare da su.

Lauyansa Jocamey Haba ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP cewa, wasu mutane dauke da makamai ne suka fitar da wanda nake karewa daga gidan yari, ba tare da son ransa ba.

"Har yanzu ina ganin an yi garkuwa da shi, yana da yakinin adalcin kasarsa, shi ya sa ba zai taba yunkurin tserewa ba," in ji shi, yayin da yake magana kan shari'ar da ake yi a halin yanzu.

Moussa Dadis Camara.
Moussa Dadis Camara. (Photo : Laurent Correau / RFI)

Lauyan as ya bayyana cewa "rayuwarsa na cikin hadari."

Harin ya girgiza Kaloum, gundumar fadar shugaban kasa, cibiyoyi kasuwanci da ofisoshin jakadanci da dama, har ma da gidan yari.

Wani jami'in filin jirgin da ke nesa da cibiyar, ya nuna cewa jiragen ba su tashi da safiyar Asabar ba, saboda ma'aikatan kula da zirga-zirgar jiragen ba su iya isa filin jirgin daga Kaloum, inda suka saba kwana.

Wasu daga cikin tsofin jami'an gwamnatin Moussa Dadis Camara.
Wasu daga cikin tsofin jami'an gwamnatin Moussa Dadis Camara. (Photo : Laurent Correau / RFI)

Kasar Guinea, wacce ke da tarihin siyasa mai zafi tun bayan samun 'yancin kai daga Faransa, ta shiga shekara ta biyu na wannan shari'a, wanda aka tsare Moussa Dadis Camara tun bayan fara sauraren karar a watan Satumban 2022, bisa zargin su da kisan gilla, azabtarwa, fyade da sauran sace-sacen da aka yi a ranar 28 ga Satumba, 2009 da jami'an tsaro suka yi a filin wasa na 28-Satumba da ke wajen birnin Conakry, inda dubun-dubatar masu goyon bayan 'yan adawa suka taru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.