Isa ga babban shafi

Rikicin Sudan ya yi wa tattalin arzikin kasar mummunar illa - IMF

Asusun ba da lamuni na duniya IMF, ya ce tattalin arzikin Sudan zai durkushe da fiye da kashi 18 cikin 100 a shekarar bana, sakamakon yakin da ya barke a kasar tun cikin watan Afrilun da ya gabata.

Wani yankin kudancin Khartoum babban birnin Sudan, yayin fafata wa tsakanin sojojin gwamnati da dakarun rundunar RSF da suka yi tawaye. 29 ga Mayu, 2023.
Wani yankin kudancin Khartoum babban birnin Sudan, yayin fafata wa tsakanin sojojin gwamnati da dakarun rundunar RSF da suka yi tawaye. 29 ga Mayu, 2023. AFP - -
Talla

IMF ya yi gargadin ne a cikin rahoton halin da tattalin arzikin duniya ke ciki, wanda ya saba fitarwa duk bayan watanni shidda, inda ya ce kazamin rikicin da ya barke a Sudan ya kassara ababen more rayuwa a kasar.

Alkaluma sun nuna cewar tun kafin barkewar rikicin Sudan sai da al’ummar kasar suka fuskanci hauhawar farashin kayayyaki har sau uku, lamarin da ya kara tabarbarewa tun cikin watan Afrilu.

Noma, wanda ke cikin muhimman sassan da ke sama wa Sudan kashi 40 cikin 100 na kudaden shiga, da kuma kashi 80 cikin 100 na guraben ayyukan yi, shi ma a halin yanzu ya durkushe sakamakon kazamin rikicin da kasar ta fada.

A ranar 15 ga watan Afrilun da ya gabata, kazamin fada ya barke tsakanin sojojin gwamnati masu biyayya ga shugaba Janar Abdel Fattah al-Burhan da kuma dakarun rundunar kai daukin gagggawa ta RSF karkashin Janar Mohamed Hamdane Dagalo, tsohon mataimakin shugaban.

A halin da ake ciki, rikicin yayi sanadin mutuwar mutane sama da 9,000 tare da raba fiye da mutane miliyan 5 da muhallansu a kasar ta Sudan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.