Isa ga babban shafi
Sudan - Tattalin Arziki

Aiwatar da manufofin IMF ya janyo zanga-zanga a Sudan

Daruruwan mutane sun gudanar da zanga-zanga a ranar Laraba a birane da dama na kasar Sudan, inda suke kira ga Firaministan kasar ya yi marabus saboda sauye-sauyen da Asusun Lamuni na duniya IMF ya tilastawa gwamnatinsa aiwatarwa.

'Yan kasar Sudan a birnin Khartoum yayin zanga-zangar adawa da matakan da gwamnati ke dauka kan tattalin arzikin kasar bisa shawarar asusun bada lamuni na IMF.  30/6/2021.
'Yan kasar Sudan a birnin Khartoum yayin zanga-zangar adawa da matakan da gwamnati ke dauka kan tattalin arzikin kasar bisa shawarar asusun bada lamuni na IMF. 30/6/2021. AFP via Getty Images - ASHRAF SHAZLY
Talla

Kwana daya kafin wannan zanga-zangar, asusun na IMF ya sanar da bai wa Sudan rancen dala bilyan biyu da milyan 500, abin da masu zanga-zangar ke cewa yunkuri ne na durkusar da kasar.

Asusun IMF, ya sanar da hakan ne bayan cimma jituwa da kasashe 101 da za su samar da wadannan kudade ga kasar ta Sudan.

A daidai lokacin da Sudan ke fama da matsin tattalin arziki wani kalubale dake gaban gwamnatin kasar kuma shi ne daukar nauyin dubban 'yan gudun hijirar da suka tsrewa tashin hankali a yankin Tigray mai fama da rikici, abinda ya sa a cikin watan Nuwamban shekarar 2020, Majalisar Dinkin Duniya ta ce Sudan din na bukatar akalla dala miliyan 150 domin taimakawa yan gudun hijirar. kasar ta Habasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.