Isa ga babban shafi

Air France ya sake tsawaita wa'adin dakatar da zirga-zirgar jiragensa a Sahel

Kamfanin sufurin jiragen sama na Air France ya sake tsawaita dakatarwar da ya yi wa zirga-zirgar jiragensa a kasashen yankin Sahel zuwa nan da karin mako guda.

Jirgin kamfanin jiragen Air France mallakin Faransa.
Jirgin kamfanin jiragen Air France mallakin Faransa. © AFP - CHRIS DELMAS
Talla

Wannan ne karo na 4 da kamfanin na Air France ke kara wa'adin dakatar da zirga-zirgar jiragen na sa a kasashen Burkina Faso da Mali, yayinda ya ki cewa komai game da dakatar da sufurin jiragensa a Nijar.

Jirgin na Air France da ke matsayin babbar hanyar sufuri tsakanin kasashen Afrika da nahiyar Turai musamman daga yankin na Sahel inda ya ke yin akalla zirga-zirga 7 cikin mako guda daga Bamako zuwa Paris kana sau 5 cikin mako guda daga Ougadougou sannan sau 4 a mako daga Niamey.

Tun a ranar 7 ga watan Agustan da ya gabata ne, kamfanin ya dakatar da zirga-zirgarsa a kasashen 3 bayan juyin mulkin Nijar na ranar 26 ga watan Yuli.

Kafin wannan sanarwa ta yau juma’a, kamfanin a baya ya ce zai dawo da zirga-zirgar jiragen nasa a ranar 4 ga watan nan amma ya dage saboda wasu dalilai, inda a yanzu kuma ya ce sai nan da ranar 24 ga watan nan.

Kamfanin ya ce, ko bayan dawo da aikin nasa a ranar 24 ga watan nan, jiragensa za su rika ratsa sararin samaniyar Nijar ne kadai ba tare da yada zango a cikin kasar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.