Isa ga babban shafi

Al'ummar Zimbabwe na kada kuri'a a babban zaben kasar

A yau Laraba ne al’ummar Zimbabwe ke kada kuri’a a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisa da ke zuwa a cikin wani mawuyacin hali na tabarbarewar tattalin arziki. An yi hasashen zai zama mai cike da kalubale, yayin da ake ganin jam'iyyar adawa za ta kwashe kuri'un matasa, sai dai har yanzu jam'iyyar ZANU-PF ce ke kan gaba a zaben.

Shugaba Emmerson Mnangagwa kenan, lokacin da ya kada kuri'arsa a makaranta firamare ta Sherwood da ke Kwekwe, Zimbabwe, 23 ga Agusta, 2023.
Shugaba Emmerson Mnangagwa kenan, lokacin da ya kada kuri'arsa a makaranta firamare ta Sherwood da ke Kwekwe, Zimbabwe, 23 ga Agusta, 2023. REUTERS/ - SIPHIWE SIBEKO
Talla

Akwai 'yan takara 11 da ke neman kujerar shugaban kasa a zaben na yau da wakilan kungiyoyi daban daban na duniya ke sanya ido a kai.

Shugaban jam'iyyar ZANU-PF mai mulki Emmerson Mnangagwa mai shekaru 80 da haihuwa, yana adawa da Nelson Chamisa, mai shekaru 45 lauya kuma Fasto da ke jagorantar jam'iyyar adawa ta CCC.

An yaba wa Mnangagwa a matsayin shugaba na gaskiya jim kadan bayan hawansa mulki, sai dai ya samu ‘yar karamar nasara a zaben 2018 a kan Chamisa, wanda har yanzu ake ganin shi ne mai kalubalantar sa a karo na biyu.

Zaben na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da tabarbarewar tattalin arziki da hauhawar farashin kayayyaki.

Ana zargin gwamnati da yi wa mulkin dimokuradiyya karan-tsaye bayan zartar da wani kudirin doka da ake kira Patriotic Bill, wanda 'yan adawa ke cewa ya saba wa ka’ida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.