Isa ga babban shafi

Al'ummar Zimbabwe sun shirya zabar wanda zai rike shugabancin kasar

Fiye da mutane 10,000 da yawancinsu sanye da riga launin ruwan rawaya, suka yi fitar dango, domin nuna goyon bayansu ga madugun 'yan adawa na Zimbabwe, Nelson Chamisa, gabanin zabukan da za a yi a kasar.

Magoya bayan madugun 'yan adawa Nelson Chamisa na jam'iyyar MDCP da ke rera waka da rawa a a wajen hedikwatar jam'iyyar bayan babban zaben kasar da aka gudanar a birnin Harare na kasar Zimbabwe, ranar 31 ga Yuli, 2018.
Magoya bayan madugun 'yan adawa Nelson Chamisa na jam'iyyar MDCP da ke rera waka da rawa a a wajen hedikwatar jam'iyyar bayan babban zaben kasar da aka gudanar a birnin Harare na kasar Zimbabwe, ranar 31 ga Yuli, 2018. REUTERS/Mike Hutchings
Talla

Zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin kasar da za a yi a ranar Laraba na da matukar muhimmanci wajen tantance makomar kasar da ke kudancin Afirka mai dimbin albarkatun ma'adinai da kasar noma.

Kasar da ke da yawan mutane masu ilimi amma babu aikin yi, na fama da matsin tattalin arziki.

Ko da yake abun ba haka yake ba a shekaru biyar da suka gabata, lokacin da Zimbabwe ta shirya gudanar da zabenta na farko tun bayan juyin mulkin da ya kawo karshen mulkin da ake masa kallon na danniya na shekaru 37 da tsohon Shugaba Robert Mugabe ya diba yana yi.

Daruruwan jama'a sun yi cunkoso kan tituna domin nuna bacin ransu na neman sauyi a kasar mai mutane miliyan 15.

Tsohon mataimakin shugaban kasar Mugabe, Emmerson Mnangagwa, ya karbi ragamar shugabancin kasar bayan juyin mulkin, ya kuma yi alkawarin bunkasar tattalin arziki kasai, da bayar da 'yancin fadin albarkacin baki, da sassauta takurawar da ake yi wa 'yan adawar da ke magantuwa kan wa'adin mulkin Mugabe, da kuma tabarbarewar dangantaka da kasashen yammacin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.