Tawagar Turai da ke sa ido a zaben Zimbabwe ta musanta labarin zargin hannu a badakalar rashawa
Tawagar Tarayyar Turai da ke sa ido kan zabukan kasar Zimbabwe a yau Asabar ta musanta labarin da wata jarida mallakar gwamnatin kasar ta wallafa na zargin cewa suna da hannu a badakalar cin hanci.
Wallafawa ranar:
A ranar 23 ga watan Agusta za a gudanar da zabukan shugaban kasa, 'yan majalisa da wakilan kananan hukumomi.
Jaridar The Herald daily a kasar ta Zimbabwe a ranar Juma'a ta ruwaito cewa wata tawagar kafofin yada labarai ta Tarayyar Turai ta gana da 'yan jarida 18 tare da raba barasa da kayan abinci da nufin 'yan jarida su yi ikirarin wuce gona da iri ga tsarin zaben da ya gudana a wannan kasa.
Sai dai shugaban tawagar ta Turai Fabio Massimo Castaldo da yake ambato wasu majiyoyi da ba a bayyana sunayensu ya yi mamakin irin zarge-zargen batanci da aka buga a cikin kafofin yada labaran Zimbabwe, ya na mai bayyana cewa “Wadannan zarge-zargen sun samo asali ne daga jita-jita da ba su da tushe, kuma kage ne gaba daya.”
Ya bayyana yunƙurin da aka yi a baya na bata sunan manufar wannan tawaga, ya kuma ƙarasa da cewa irin waɗannan labaran ba su dace ba a wannan lokaci da ake fatan cimma zaman lafiya mai dorewa a wannan kasa ta Zimbabwe, da kuma ganin kokarin da kungiyar Tarrayar Turai ke yi ta fuskar kawo nata kokari domin tabbatar da sahihancin wannan zabe.
Sauran wadanda suka kasance ‘yan sanya ido a zaben sun hada da kungiyar Tarayyar Afirka, da Commonwealth da kuma kungiyar raya kasashen kudancin Afirka (SADC). 'Yan takara 12 ne dai suka fafata a zaben shugaban kasa, zaben da ake kyautata zaton Shugaba mai ci Emmerson Mnangagwa mai shekaru 80 da Nelson Chamisa mai shekaru 45 su kasance a zagaye nag aba har idan ta kama a wannan kasa da ke fama da matsalar cin hanci da rashawa da hauhawar farashin kayayyaki da fatara da kuma rashin aikin yi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu