Isa ga babban shafi

Zimbabwe ta gudanar da taron jana'iza na musamman ga Sarauniyar Ingila

Babbar majami’ar Zimbabwe ta gudanar da gagarumin taron jana’iza na musamman ga Sarauniyar Ingila Elizabeth ta 2 wadda ta mutu cikin makon jiya ta na da shekaru 96.

Akwatin gawar Sarauniya Elizabeth ta biyu.
Akwatin gawar Sarauniya Elizabeth ta biyu. AP - Nariman El-Mofty
Talla

Kafofin yada labaran Zimbabwe sun ruwaito yadda Babban limamin cocin kasar Bishop Farai Mutamiri ya jagoranci zaman jana’izar da addu’o’i a majami’ar Anglican da ke Harare babban birnin kasar.

Zaman jana’izar na musamman ya hada da fararen fata galibi ‘yan Ingila da ke zaune a kasar ciki har da jakadan Birtaniya a Zimbabwe sai kuma dubunnan ‘yan kasar da suka halarci cocin don addu’o’I ga Sarauniya Elizabeth.

A jawabin bayan kammala taron jana’izar Bishop Farai Mutamiri ya ce sun gudanar da addu’o’in samun rahama ga Sarauniya Elizabeth ta 2 yayinda suka yi wasu addu’o’in na musamman ga Sabon Sarki Charles na 3 dama sauran ilahirin iyalan gidan sarautar Birtaniya.

Bishop Farai ya kuma yi amfani da damar wajen mika sakon ta’aziyyar Zimbabwe ga ilahirin al’ummar Birtaniya da sauran kasashe rainon Ingila, inda ya ce Mutuwar Sarauniyar babban gibi ga Duniya.

Jakadan Birtaniya a Zimbabwe Melanie Robinson ta ce manufar taron jana’izar shi ne godiya da kuma jinjin aga sarauniyar wadda ta sadaukar da ilahirin rayuwarta wajen hidimtawa ba kadai Birtaniya ba har ma da sauran kasashen Duniya musamman rainon Ingila.

A litinin mai zuwa ne ake saran birne Sarauniya Elizabeth ta 2 bayan kammala mata jana’izar karshe da za ta samu halartar manyan shugabannin, ‘yan siyasa da masu rike da sarautun gargajiya daga sassa daban-daban na Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.