Isa ga babban shafi

Saudiyya ta kame mutumin da ya yi wa Sarauniyar Ingila aikin Umrah

Mahukuntan Saudiyya sun kame wani mutum wanda ya yi tattaki daga Yemen don yiwa Sarauniyar Ingila Elizabeth ta 2 aikin Umrah da nufin samun rahamar ubangiji.

Sarauniyar Ingila, Elizabeth ta 2.
Sarauniyar Ingila, Elizabeth ta 2. AP - Alastair Grant
Talla

Mutumin dan kasar Yemen da ba a bayyana sunan shi ba, ya wallafa wani gajeran bidiyo a dandalin sada zumunta wanda ya nuna shi a gaban dakin ka’aba yana addu’o’in neman rahama ga Sarauniyar wadda ta mutu ranar 9 ga watan da muke ciki na Satumba ta na da shekaru 96.

Bidiyon ya nuna mutumin rike da wani allo mai dauke da rubutun ‘ibadar aikin umrah ga Sarauniya Elizabeth da fatan Allah ya karbe ta a cikin salihan bayi’, bidiyon da ya karade shafukan sada zumunta.

Tuni dai wannan bidiyo ya haddasa cece-kuce yayinda mutane suka rika kiraye-kirayen ganin lallai mahukuntan kasar sun kame mutumin tare da hukunta shi.

Bisa dokokin Saudiyya dai, babban laifi ne gudanar da aikin hajji ko umrah rike da wani allon bayanai kan wani mutum ko kuma furta wasu kalamai da ba Kalmar Allah ba.

Haka zalika duk da cewa addinin Islama ya halatta yiwa matattu aikin hajji ko Umrah, amma hakan baya halatta ga wanda ba musulmi ba.

Jami’an tsaron Harami sun kame mutumin wanda suka ce zai fuskanci hukunci dai dai da laifinsa, sai dai basu bayar da bayani kan shekarunsa da kuma dalilinsa na aikata hakan ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.