Gawar Sarauniya Elizabeth ta bar fadar Balmoral zuwa Edinburgh
Tafiya daga Balmoral zuwa Fadar Holyroodhouse a Edinburgh na da nisan mil 175. Akwatin gawar sarautar na tafiya ne tsakanin Aberdeen da Dundee, a gabar gabashin Scotland.
Wallafawa ranar:
Ayarin motocin rakiyar sun ketare garin Angus na Forfar inda suka wuce fadar Glamis Castle, gidan kakannin mahaifiyar marigayiya Sarauniya kuma wurin da aka ce ta gudanar da rayuwar yarinta
A nan ne iyayenta suka gudanar da hutun aure, kuma mahaifiyarta, Sarauniya Elizabeth, ta haifi 'yar uwarta Gimbiya Margaret a 1930.
Akwatin gawar Sarauniyar zai wuce ta Edinburgh a yau zuwa Fadar Holyroodhouse.
A halin da ake ciki a Ingila, mutane na ci gaba da tururuwa zuwa fadar Windsor da fadar Buckingham domin shimfida furanni da ke nuna alhinin tafiyar Sarauniyar.
Ana bukukuwan shelanta sabon sarki a fadin Birtaniya
Yayin da aka dauko gawar sarauniya daga Balmoral zuwa Holyroodhouse, ana gudanar da bukukuwa na musamman da kuma fareti a Wales, Scotland da Ireland ta Arewa domin shelar Sarki Charles III.
Yanzu haka dai an karanta sanarwar nadin sabon sarki a Cardiff, Edinburgh da Belfast.
Bayan haka, za a harba bindigogi 21 a wajen fadar Edinburgh, fadar Cardiff da kuma fadar Hillsborough a Belfast.
Dubban mutane ne suka taru a dukkannin wurare ukun, domin shaida yadda ake bikin hawan sabon sarkin Birtaniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu