Isa ga babban shafi

Akwatin gawar Sarauniya Elizabeth ya isa Edinburgh

Akwatin gawar Sarauniya ya isa Edinburgh, bayan tafiyar sa'o'i shida, yayin da dubban mutane suka yi dafifin yi mata bankwana a Royal Mile da ke birnin.

Marigayiya Elizabeth ta biyu
Marigayiya Elizabeth ta biyu © AP - Danny Lawson
Talla

Tawagar da ta dauko akwatin gawar ta yi tafiyar sa'o'i shida daga fadar Balmoral, inda za ta yi kwanaki biyu a fadar Holyroodhouse.

A ranar Talata ne za a kai akwatin gawar zuwa Landan, kuma Sarauniyar za ta kwana a Westminster daga ranar Laraba.

Za a yi jana'izar Sarauniyar a Westminster Abbey ranar Litinin 19 ga Satumba, kuma ranar za ta kasance ranar hutu a fadin Birtaniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.