Isa ga babban shafi

Zimbabwe ta yi afuwa ga kashi 1 bisa 5 na fursunonin kasar

Gwamnatin Zimbabwe ta yi afuwa ga kaso 1 bisa 5 na fursunonin kasar a wani yunkuri na rage cunkoso, dai dai lokacin da ya rage watanni kalilan a gudanar da babban zaben kasar.

Fursinoni fiye da dubu 4 Zimbabwe ta yiwa afuwa don rage cunkoso.
Fursinoni fiye da dubu 4 Zimbabwe ta yiwa afuwa don rage cunkoso. AP - TSVANGIRAYI MUKWAZHI
Talla

Wata sanarwa da hukumar da ke kula da gidajen yarin Zimbabwe ta fitar ta ce anyi afuwa ga fursunoni dubu 4 da 270 adadi mai yawa da kasar ta tabar fitarwa daga gidan yari a lokaci guda.

Sanarwar gidan yarin ta bukaci al’ummar kasar su karbi tsaffin fursunonin don basu damar ci gaba da rayuwa a cikin jama’a lura da cewa basu aikata manyan laifukan da za su hanasu komawa rayuwarsu ta baya ba.

Wannan mataki na gwamnati ya rage cunkoson gidajen yarin da Zimbabwe ke fama da shi a gidajen tsare masu laifi 50 da ke sassan kasar masu karfin daukar mutane dubu 17 amma kuma ake tsare da mutanen da yawansu ya haura dubu 22 gabanin yin afuwar.

Kakakin hukumar kula da gidajen yarin a Zimbabwe Meya Khanyezi ta shaidawa AFP cewa babbar manufar afuwar wadda shugaban kasa Emmerson Mnangagwa ya umarta shi ne rage cunkoso.

Jami’ar ta ce afuwar ta shafi rukuni da dama na fursunonin musamman wadanda shekarunsu suka yi nisa sai kuma wadanda suka kammala kash1 3 bisa hudun wa’adinsu a gidan yarin.

Shirin afuwar dai bai shafi wadanda aka daure da manyan laifukan da suka kunshi fashi da makami ko kisan kai ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.