Isa ga babban shafi

Cutar kyanda ta kashe sama da mutum 600 a kasar Zimbabwe

Ya zuwa yanzu annobar cutar kyanda a Zimbabwe ta lakume rayukan mutane 685, fiye da sau hudu da aka samu rahoton bullar cutar a kusan makwanni biyu da suka gabata ko da yake ana ci gaba da yin allurar rigakafin cutar a fadin kasar.

Cutar kyanda dai na matukar yin illa ga yara kanana
Cutar kyanda dai na matukar yin illa ga yara kanana REUTERS - HEREWARD HOLLAND
Talla

Kasar Zimbabwe tana da mutane 6,034 da aka tabbatar sun harbu da cutar, wadanda suka hada da yara 4,266 da kuma mutum 685 da suka mutu," in ji ma'aikatar lafiya ta shafin Twitter, inda ta ce an samu sabbin alkaluman mutum 191 daga cikin su 37 sun mutu ne a ranar 1 ga Satumba.

Da farko dai yara ‘yan tsakanin watanni shida zuwa shekaru 15 ne ke kamuwa da cutar, musamman ma wadanda suka fito daga bangaren masu tsatssauran ra’ayi da ba su yarda da allurar rigakafi ba, in ji ministar yada labaran kasar Monica Mutsvangwa.

A cewar gwamnati, wasu kungiyoyin addinai ba su yarda da allurar rigakafin ba kuma sun dogara ne da addu'a.

Ko da yake har yanzu shugabannin coci-coci ba su mayar da martani ga ikirarin gwamnati na cewa imaninsu ne ke da alhakin yaduwar cutar kyanda ba.

Sai dai Mutsvangwa  ta ce gwamnati na tuntubar shugabannin addini don samun tallafi da wayar da kan jama'a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.