Kenya: Shugaba Ruto ya gargadi jagoran 'yan adawa a kan tsaron kasa
Shugaban Kenya, William Ruto ya ce ba zai nemi amincewar abokin hamayyarsa a kan abin da ya shafi tsaron kasar ba, biyo bayan amincewa da zama a teburin tattaunawa da zummar kawo karshen mummunar zanga-zangar adawa da gwamnatinsa.
Wallafawa ranar:
Ruto ya ce zai rungumi tattaunawa, amma yana mai gargadin abokin hamayarsa cewa ba zai lamunci wata zanga-zanga da za ta jefa rayuwa da kadarorin al’umma cikin hadari ba.
Tun a watan Maris Jagoran ‘yan adawa, Raila Odinga ya shirya zanga-zangar kwanaki 9 don nuna rashin amincewa da abin da ya kira gwamnati mara halasci, wadda ta jefa kasar cikin haali na matssin tattalin arziki.
A ranar Asabar, bangaren gwamnati da na ‘yan adawa suka sanar da aniyarsu ta warware rikicin da ke tsakaninsu cikin ruwan sanyi, biyo bayan zanga-zangar da ‘yan adawa suka shirya, wadda ta yi sanadin mutuwar mutane 20.
Kasancewar Kenya daya daga cikin kasashen da dimokaradiyya ta samu ginndin zama a nahiyar Afrika, tashin hankalin da kasar ta fuskanta ta janyo kiraye-kirayen sasantawa daga ciki da wajen kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu