Isa ga babban shafi

An sake arangama tsakanin masu zanga-zanga da jami'an tsaron Kenya

Jami’an ‘yan sandan Kenya sun yi amfani da hayakin mai sanya hawaye tare da ruwan zafi don tarwatsa dandazon masu zanga-zangar adawa da matsin rayuwa, boren da jagoran adawa Raila Odinga ke jagoranta duk da haramcin da hukumomi suka yi kan gangamin nay au litinin.

Masu zanga-zanga a birnin Nairobi na Kenya.
Masu zanga-zanga a birnin Nairobi na Kenya. AP - Brian Inganga
Talla

Zanga-zangar ta yau litinin karkashin jagorancin jagoran adawa Raila Odinga na zuwa ne duk da haramcin da rundunar ‘yan sandan Kenya ta yi a jiya lahadi, bayan da babban sufeton ‘yan sandan kasar Japhet Koome ya bayyana cewa gangamin ba komi zai haifar ba face tashin hankali lura da yadda makamancin boren na makon jiya ya haddasa asarar rai.

Rundunar ‘yan sandan ta Kenya ta ce gangamin da ke gudana  a yammacin birnin Kisumu haramtacce ne.

Raila Odinga dai ya bukaci gudanarr da zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa sakamakon tashin farashin kayaki a dukkanin ranakun litinin da Alhamis don tilastawa gwamnatin shugaba William Ruto daukar mataki don saukakawa jama’a.

Sai dai a makon jiya an yadda zanga-zangar ta juye zuwa rikici bayan arangama tsakanin masu boren da jami’an tsaron wanda ya kai ga jikkatar dukkanin bangarorin biyu tare da kame wasu mutane akalla 400 baya kisan wani dalibin jami’a guda a birnin Nairobi.

Tun da safiyar yau litinin aka baza jami’an tsaro a manyan titunan kasar don kange masu boren daga amsa kiran Odinga wajen fita zanga-zangar sai dai duk da haka an ga fitar jama’a musamman a Kisumu yankin da Raila Odinga ke da tulin magoya baya.

Yayin zanga-zangar dai Odinga ya gabatar da jawabi gaban magoya bayansa dangane da halin da Kenya ta fada saboda tsadar rayuwa inda ya bukaci lallai jama’a su fito su nemi hakkinsa, jawabin da ya gudana gabanin jami’na tsaro su afka mus uta hanyar feshin ruwan zabi da barkonon tsohuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.