Isa ga babban shafi

Mutane uku daga cikin masu zanga-zangar Kenya sun rasa rayuwarsu - 'Yan sanda

Akalla mutane uku suka mutu daga cikin wadanda suka gudanar da zanga-zanga a Kenya, kamar yadda wani jami'in asibiti da jami'an 'yan sanda suka shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP.

Akalla mutane uku suka mutu daga cikin wadanda suka gudanar da zanga-zanga a Kenya
Akalla mutane uku suka mutu daga cikin wadanda suka gudanar da zanga-zanga a Kenya REUTERS - THOMAS MUKOYA
Talla

Dama dai jagoran 'yan adawar kasar Raila Odinga ne, ya bukaci 'yan kasar su fito domin nuna adawa da karin haraji da gwamnatin ta yi.

A lokacin zanga-zangar ta ranar Juma’a, jami’an ‘yan sanda sunyi amfani da hayaki mai sa hawaye, wajen tarwatsa masu zanga-zangar a babban birnin kasar Nairobi, da kuma daukar irin wannan mataki a biranen Mombasa da kuma Kisumu.

Ko a jiya asabar sai da jami’an ‘yan sanda suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa wakilan kungiyoyin fararen hula, ciki kuwa harda tsohon alkalin alkalai Willy Mutunga, da ke neman a sake tarin mutanen da aka kama a lokacin zanga-zangar da suka gudanar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.