'Yan sandan Kenya sun harba hayaki mai sa hawaye kan masu zanga-zanga
'Yan sandan Kenya sun harba hayaki mai sa hawaye kan tawagar madugun 'yan adawar kasar Raila Odinga a jiya Juma'a, ya yin da kungiyoyin kare hakkin dan adam suka yi tir da kamen da jami’an tsaro suka yi ba bisa ka'ida ba, a lokacin zanga-zangar adawa da gwamnati kan tsadar rayuwa da kuma karin harajin da ta yi.
Wallafawa ranar:
A cewar wakilin kamfanin dillancin labaran Faransa AFP, an harba hayaki mai sa hawaye kan ayarin motocin Odinga ne bayan da ya yi wa masu zanga-zangar jawabi a babban birnin kasar Nairobi.
'Yan sanda sun kuma dauki irin wannan mataki na tarwatsa masu zanga-zanga a birnin Mombasa da Kisumu.
Wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP ya kuma bayyana cewa 'yan sanda sun yi kame a birnin Nairobi, inda aka tsaurara matakan tsaro a game da zanga-zangar da Odinga ya kira don nuna adawa da manufofin gwamnatin shugaba William Ruto.
A wajen gangamin, Odinga ya bayyana shirin tattara sa hannun mutane miliyan 10 a yunkurin tsige shugaba Ruto da ke zaman babban abokin hamayyarsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu