Isa ga babban shafi

Raila Odinga ya yi watsi da sakamakon zaben shugabancin kasar Kenya

Dan takarar shugaban kasar Kenya Raila Odinga da ya sha kaye ya sha alwashin bin dukkan hanyoyin tsarin mulki da na doka bayan ya ki amincewa da sakamakon zaben da ya baiwa abokin hamayyarsa William Ruto nasara.

Dan takara shugabancin kaasr Kenya kenan, Raila Odinga yayin da yake gabatar da jawabi a wani taron manema labarai ranar 16 ga Agusta, 2022.
Dan takara shugabancin kaasr Kenya kenan, Raila Odinga yayin da yake gabatar da jawabi a wani taron manema labarai ranar 16 ga Agusta, 2022. AP - Ben Curtis
Talla

Ruto mai shekaru 77 da haihuwa wanda ya kasance gogaggen dan siyasa ya bayyana sakamakon zaben da aka gudanar a ranar 9 ga watan Agusta a matsayin magudi, inda ya bayyana karara cewa zai mika korafin sa gaban kotun kolin kasar.

Odinga narrowly lost his fifth bid for the top job to Deputy President Ruto, who was proclaimed president-elect Monday after a nail-biting wait for results.

Odinga ya sha kaye a zaben karo na biyar kenan da yake neman kujerar shugabancin kasar inda a wannan karo ya sha kaye a hannun mataimakin shugaban kasar Ruto, wanda aka ayyana a matsayin zababben shugaban kasa a ranar litinin.

Magoya bayansa sun yi ta kururuwa kan sakamakon, wanda kuma ya haifar da rarrabuwar kawuna a hukumar zabe mai zaman kanta ta IEBC wadda ta fitar da sakamakon.

Ana dai kallon sakamakon zaben a matsayin wani gagarumin ci gaba da aka samu ga tsarin dimokuradiyya a yankin gabashin Afirka, bayan rikicin  da aka tafka zabukan da suka gabata sakamakon zargin magudi da zubar da jini.

Odinga ya sha kaye da kuri’u kusan 230,000 duk da goyon bayan tsohon abokin hamayyarsa, shugaba mai barin gado Uhuru Kenyatta, da kuma karfin goyon bayan da ya samu daga  jam’iyya mai mulki.

Babu wani sakamakon zaben shugaban kasa da bai kai ga gaci ba a Kenya tun shekara ta 2002, ko da yake Odinga ya ce anyi masa magudi a zaben 2007, 2013 da 2017.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.