Isa ga babban shafi

'Yan gudun hijirar Sudan na kwarara zuwa tsakiyar Afirka - MDD

Majalisar Dinkin. Duniya, ta ce, mutanen da rikici ya tilasta mus tserewa daga kasar Sudan, yanzu haka na neman mafaka a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana dakon karin wasu 'yan gudun hijirar da ke tunkarar kasar yanzu haka
Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana dakon karin wasu 'yan gudun hijirar da ke tunkarar kasar yanzu haka © UNHCR
Talla

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD, ta ce tana kokarin yadda za ta gyarawa dubban ‘yan gudun hirar masauki, kafin ruwan sama ya kankama.

Kafin nan, UNHCR tare da hukumar samar da abinci ta duniya na kokarin gina gidaje, bandakuna da kuma ruwan da za su wadata ‘yan gudun hijira 14,000 da suka isa kasar ta Congo.

Bobo Kitoko, babban jami’in bangaren da ya shafi adana bayanai na UNHCR, y ace ana bukatar isasshen abinci, matsuguni da kuma ruwa.

MDD ta ce, da dama daga cikin wadanda suka isa kasar mata ne da kananan yara, da suka fito daga Nyala da ke Sudan din, wadanda suka fuskanci barazana daga masu dauke da makamai, cin zarafi da sauransu.

A watan jiya ne, aka fara tantance ‘yan gudun hijirar, kuma ana ci gaba da yi, yayin da daruruwan mutane ke ci gaba da tsallakawa zuwa iyakar Chadi.

UNHCR ta ce, jami’an bada agajin gaggawa na ci gaba da bawa ‘yan gudun hijirar kulawar da ta dace, musamman kana bin da ya shafi batun lafiyarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.