Isa ga babban shafi
Majalisar Dinkin Duniya

Mutane miliyan 56 na fama da karancin abinci mai gina jiki

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana samun karuwar mutanen da ke fama da karancin abinci mai gina jiki a kasashen Afghanistan da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo da Sudan ta kudu da kuma Yemen a shekarar da ta gabata, sakamakon karuwar tashe-tashen hankula, matakin da ke danganta tashin hankali da karancin abinci.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya babban abin da zai kawo karshen matsalar yunwar da duniya ke fuskanta shi ne kawo karshen yake-yaken da kasashe ke fuskanta.
A cewar Majalisar Dinkin Duniya babban abin da zai kawo karshen matsalar yunwar da duniya ke fuskanta shi ne kawo karshen yake-yaken da kasashe ke fuskanta. Reuters
Talla

Majalisar ta ce, yayin da wadannan kasashe biyar ke fama da matsala, cigaba aka samu a Somalia da Syria da kasashen da ke Yankin Tafkin Chadi saboda ingantuwar tsaro.

Rahotan hadin gwuiwa da hukumar samar da abinci ta Majalisar da hukumar bunkasa noma suka fitar, ya ce wasu mutane miliyan 56 daga kasashe 8 ke bukatar agajin abincin gaggawa saboda tashin hankalin da ake samu a yankunan su.

Jose Graziano da Silva, Daraktan hukumar noma da samar da abinci ya ce binciken na su ya dada nuna yadda tashin hankali ke matukar illa kan rayuwar miliyoyin mutane da suka hada da mata da maza da yara.

David Bearsley, shugaban hukumar samar da abinci, ya ce Majalisar na bukatar hanyar shiga sassan da ake samun tashin hankali domin kai dauki.

Jami’in ya ce babban abinda duniya ke bukata shi ne kawo karshen yake- yaken da ake samu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.