Hadarin mota ya ritsa da mutane 24 a Zambia
A Zambia akalla mutane 24 da ke karkashin wata mujami’a suka rasa rayukan su sanadiyyar hadarin mota.
Wallafawa ranar:
Hukumar yan Sanda da ta isa yankin mai suna Chongwe da ke da nisan kilometa 42 da babban birnin kasar Lusaka a kan hanyar su ta zuwa lardin Siavonga mai nisan kilometa 195 da Lusaka,yan sanda sun bayyana cewa motar na dauke da mutane 35,motar ta yi tawo mu gama da wata babbar mota,inda nan take mutane 24 da suka hada da mata 23 da wani namiji suka rasa rayukan su a cewar kakkakin yan sanda Danny Mwale.
Kasar Zambia ta yi kaurin suna a fanin da ya shafi haduran mota sabili da rashin wadatatun hanyoyi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu