Isa ga babban shafi
ZABEN-ZAMBIA

'Yan Zambia zasu shaki iskar 'yanci - Hichilema

Sabon Shugaban kasar Zambia Hakainde Hichilema yayi alkawarin gina tattalin arzikin kasar da kuma yaki da talaucin da ya addabi jama’a tare da hada kan jama’a.

Sabon shugaban Zambia Hakainde Hichilema
Sabon shugaban Zambia Hakainde Hichilema © REUTERS/Mike Hutchings
Talla

Yayin da yake jawabi bayan ya karbi rantsuwar kama aiki a gaban dubban jama’ar kasar, Hichilema ya sha alawashin kaddamar da shirin ceto tattalin arzikin Zambia domin fitar da dubban jama’a cikin talaucin da suke fama da shi.

Shugaban ya kuma bayyana aniyar sa ta mutunta hakkokin Bil Adama sabanin yadda aka gani a lokacin mulkin Edgar Lungu da ya gabace shi.

Hichilema ya shaidawa mahalarta bikin cewar Zambia ta nunawa duniya ci gaban dimokiradiyar kasar wanda ya kaiga samun mika mulki tsakanin zababbun shugaban kasa har sau 3 tun da aka fara amfani da jam’iyyun siyasa da yawa a cikin kasar.

Shugaban yace zasu mayar da hankali wajen bunkasa noma da kuma hakar ma’adinai, yayin da yace gwamnatain sa ba zata amince da cin zarafin jama’a da kuma bangancin siyasa ba.

A karshe shugaban ya shaidawa taron cewar lokaci yayi da kowanne dan kasar Zambia zai shaki iskar ‘yanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.