Isa ga babban shafi

Japan za ta taimakawa kasar Mozambique yakar ayyukan ta'addanci

Firaministan kasar Japan Fumio Kishida ya yi alkawarin taimakawa Mozambique yakar masu tayar da kayar baya da suka addabi arewacin kasar.

Firaministan kasar Japan, Fumio Kishida kenan.
Firaministan kasar Japan, Fumio Kishida kenan. AP - Efrem Lukatsky
Talla

Lardin Cabo Delgado da ke arewacin kasar Mozambique mai arzikin iskar gas na fafatawa da ‘yan tawaye karkashin jagorancin mayakan da ke da alaka da kungiyar IS.

Kasar Mozambique ta shiga yanayi na kyakkyawan fata, bayan da aka gano albarkatun dimbin iskar gas, mafi girma da aka gano a kudu da hamadar sahara, wanda aka samu a lardin arewacin kasar dake da rinjayen musulmi a shekarar 2010.

Idan har aka samu nasarar kammala aikin samar da iskar gas din, Mozambique za ta iya zama daya daga cikin kasashe goma da suka fi fitar da iskar gas a duniya, a cewar alkaluma.

Amma tashe-tashen hankula a cikin shekaru biyar da suka gabata, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 4,600, ya sanya shakku kan aikin.

Japan ita ce kasa ta farko da ta fi fitar da iskar gas zuwa kasuwar duniya, kasuwancin da ta saba rabawa da kasar China.

Firaministan na Japan, ya ce kasar sa na kokarin karfafa alakar da ke tsakaninta da Mozambique din, don haka taga ya dace ta taimakawa kasar magance matsalolin tsaron da suka addabe ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.