Isa ga babban shafi

Tsaro: Kamfanin samar da makamashi na Faransa ya dakatar da aiki a Mozambique

Katafaren kamfanin samar da makamashi na kasar Faransa Total SE ya dakatar da aikin samar da iskar gas din da ya kai dalar Amurka biliyan 20 a kasar Mozambique, sakamakon karuwar tashe-tashen hankula a yankin, ciki har da harin da mayakan da ke da alaka da kungiyar IS suka kai a watan Maris.

Tambarin kamfanin TotalEnergies kenan
Tambarin kamfanin TotalEnergies kenan REUTERS - SARAH MEYSSONNIER
Talla

Matakin dai tamkar babbar koma baya ce ga kamfanin Total, wanda ya sayi hannun jarin gudanar da aikin kan dala biliyan 3.9 a shekarar 2019, bisa fatan za a fara fitar da man da aka sarrafa a shekarar 2024, wanda zai rika fitar da ganga miliyan 13 a duk shekara kamar yadda aka tsara.

Total dai ya ci gaba da gudanar da aikin ne a watan da ya gabata, bayan da aka dakatar da shi tun watan Janairu saboda barazanar tsaro, yayin da 'yan tawaye sama da 100 suka kai farmaki garin Palma da ke kusa da wurin abin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama, tare da haifar da asarar da miliyoyin daloli.

Matsalar tsaro ta haifar da babbar koma baya ga kasar Mozambique, wadda ke fuskantar karuwar adadin mace-mace tare da raba dubban mutane da muhallansu.

Masana na ganin fitar da mai na iya taimakawa wajen sauya tattalin arzikin kasar da ta kasance daya daga cikin kasashe mafiya talauci a duniya.

Kasar Mozambique ta yi fatan samun kusan dala biliyan 100 na kudaden shiga cikin shekaru 25 daga ayyukan samar da iskar gas din.

Tuni dai jinkirin da aka samu tun da farko ya sa asusun ba da lamuni na duniya IMF ya rage hasashen ci gaban tattalin arzikin da ake ganin za ta samu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.