Isa ga babban shafi

Firaministan Japan na ziyarar aiki ta farko a Afrika

A kokarin sa na warware alkawuran da ke tsakanin kasashen Afirka da Rasha, Firaministan Japan Fomio Kishida ya fara rangadin kasashe 4 a nahiyar da kuma Singapore don tattauna batutuwa masu muhimmanci a wannan bangare, inda ya fara da kasar Masar. 

Firaministan Japan Fumio Kishida
Firaministan Japan Fumio Kishida REUTERS - ISSEI KATO
Talla

Firaministan ya fara wannan ziyarar ce ana sauran makonni 3 ya karbi bakoncin taron kasashe masu karfin tattalin arziki na G7 da zai gudana a Hiroshima. 

Ziyarar da ta kasasnce ta farko da Kishida ya yi a Afirka tun bayan da ya hau karagar mulki a watan Oktoban 2021 na zuwa ne a daidai lokacin da ake kokarin karfafa alaka da kasashe masu tasowa a yankunan da suka hada da Asiya da Afirka da kuma Latin Amurka. 

A taron G-7 da za a yi a yankin sa na Hiroshima a watan Mayu, Kishida zai nemi hadin kan kasashen duniya don marawa Ukraine baya, sakamakon mamayar da Rasha ta yi mata. Sai dai kasashe da dama a Kudancin Duniya sun ki lamuntar daukar matsaya kan yakin. 

Kishida ya tabbatar da cewa indai bangaren kudancin duniya za su ba da hadin kai akan matakan kawo karshen wannan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine to babu shakka za a samu nasarar magance matsalar ta hanyar da ta dace. 

Wasu kasashen nahiyar ta Afirka dai sun yi dogaro ne da kasashen Rasha a bangaren samun makamashi da kuma China ta bangaren tallafin tattalin arziki da saka jari. 

Bayan ziyarar Kishida a Masar, zai zarce zuwa Ghana da Kenya da kuma Mozambique, kamar yadda ya tsara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.