Najeriya ta aike da sojoji 197 don aikin wanzar da zaman lafiya a Gambia
Rundunar sojin Najeriya ta aike da dakarunta 197 Gambia domin gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya, daga cikinsu akwai manyan ofisoshi 14 da kuma sojoji 183.
Wallafawa ranar:
Wannan mataki na zuwa ne kwanaki 9 da tura wasu dakarun na daban zuwa kasar Guinea Bissau.
Dakarun wadanda tun a ranar 3 ga watan Afrilu suka soma horon shirin tafiya kasar a sansanin horas da masu aikin wanzar da zaman lafiya naMartin Luther Agwai International dake Jaji, a jihar Kaduna, sun shafe tsawon makonni 4 ana musu horo.
Yayin gabatar da jawabi ga dakarun na ECOWAS a lokacin da ake bikin kammala horon, Shugaban gudanarwar Taoreed Lagbaja ya ce aike dakarun ya kara nuna kudirin Najeriya a ayyukan tsaro da wanzar da zaman lafiya da ake gudanarwa a kasashen duniya.
Janar Lagbaja ya kuma bukaci dakarun su mayar da hankali wajen gudanar da aikin da ya kai su bil hakki a Gambia, tare da kaucewa duk wani abu da ka iya bata sunan rundunar sojin na Najeriya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu