Isa ga babban shafi

Annobar Cholera ta barke a Mozambique wata daya bayan guguwar Freddy

Bayan mummunar barnar da kakkarfar guguwar Freddy ta yi wa Mozambique a watan jiya inda ta raba mutane dubu 184 da muhallansu annobar cutar Cholera ko kuma amai da gudawa da kasar ke gani ta sake juyowa, wadda aka bayyana da mafi muni da kasar ta taba gani a cikin fiye da shekaru 10 da suka gabata.

A duk shekara Mozambique kan yi fama da annobar cutar ta amai da gudawa ko kuma Cholera sai dai a wannan karon masana sun ce za ta zama mafi muni.
A duk shekara Mozambique kan yi fama da annobar cutar ta amai da gudawa ko kuma Cholera sai dai a wannan karon masana sun ce za ta zama mafi muni. Yasuyoshi CHIBA / AFP
Talla

Hukumar lafiya ta Duniya WHO ta bayyana cewa yanzu haka fiye da mutane miliyan 1 yanzu haka na fuskantar hadarin kamuwa da cutar ta amai da gudawa.

Wakilin WHO da ya kai ziyara Maputo Dr Severin von Xylander ya ce akwai bukatar daukar matakan dakile yaduwar cutar a sassan kasar lura da yadda ake ci gaba da ganin karuwar masu kamuwa da ita.

Dr Xylander ya ce duk da yadda Mozambique ta saba ganin bullar cutar Cholera a tsakanin watannin Oktoba zuwa Aprilun kowacce shekara a wannan karon yaduwarta ta kasance mafi muni cikin shekaru 20.

Wakilin na WHO ya ce yanzu haka akwai mutane dubu 21 da suka harbu ciki har da wasu 95 da cutar ta kashe.

Wannan ibtila’I na Cholera na zuwa ne bayan guguwar Freddy ta lalata asibitoci da cibiyoyin lafiya 163 wanda ke bayyana kalubalen lafiyar da kasar za ta fuskanta a yaki da cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.