Isa ga babban shafi

Mozambique ta gano bullar cutar Polio ta farko cikin shekaru 30

Kasar Mozambique ta sanar da bullar cutar shan inna ko Polio cikinta, wadda aka gano wani yaro ya kamu da ita a yankin Tete da ke arewa maso gabashin kasar.

Wani yaro da ake yi wa rigakafin kamuwa da cutar Polio a garin Maiduguri da ke Najeriya.
Wani yaro da ake yi wa rigakafin kamuwa da cutar Polio a garin Maiduguri da ke Najeriya. © REUTERS/Afolabi Sotunde/File Photo
Talla

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce, wannan shi ne karo na farko da aka samu bullar cutar ta Polio a Mozambique cikin kusan shekaru talatin.

Hukumar ta WHO ta kara da cewar, karo na biyu kenan da cutar ke sake bayyana a kudancin Afirka cikin wannan shekara, bayan barkewar ta a Malawi cikin watan Fabrairu, inda har wani yaro ya fara samun nakasa a karshen watan Maris.

Miliyoyin yara kanana ne dai aka yi wa allurar rigakafin cutar ta Polio tare da tallafin hukumar ta WHO a fadin kudancin Afirka domin dakile yaduwar cutar a nahiyar, wadda aka ayyana kawar da ita a shekarar 2020.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.