Isa ga babban shafi

Rikici ya tilasta kananan yara dubu 34 barin muhallansu a Mozambique- Rahoto

Kungiyar agaji ta Save the Children ta ce rikicin da ke ci gaba da tsananta a sassan Mozambique ya tilastawa kananan yara fiye da dubu 34 tserewa daga muhallansu cikin watan Yuni, alkaluman da ke matsayin mafi yawa da kungiyar ta tattara a rahotonta na wata-wata.

Yankin Cabo Delgado da ayyukan ta'addanci ya tsananta a Mozambique.
Yankin Cabo Delgado da ayyukan ta'addanci ya tsananta a Mozambique. © LUSA - LUÍSA NHANTUMBO
Talla

Rahoton da kungiyar agajin ta Birtaniya ta fitar yau juma’a, ta ce alkaluman na yara dubu 34 shi ne mafi yawa na adadin kananan yaran da rikicin ya tilastawa barin muhallansu cikin wata guda a kasar ta Mozambique da ke fama da hare-haren masu ikirarin jihadi tun shekarar 2017.

Save the Children ta ce jumullar alkaluman mutanen da hare-haren ya tilastawa barin muhallansu ya kai dubu 50 a yankuna daban-daban na kasar ciki har da Cabo Delgado da hare-haren yafi tsananta, baya ga wasu mutum 53 da ‘yan ta’addan suka kashe.

Daraktar kungiyar mai kula da Mozambique Brechtje van Lith ta bayyana watan na yuni a matsayin mafi muni ga iyalai la’akari da yadda hare-haren kungiyoyin masu ikirarin jihadi ya daidaitasu.

A cewar van Lith zuwa yanzu rikicin na Mozambique ya raba mutane fiye da dubu 700 da muhallansu wadanda suka fantsamu sassan kasar don samun matsugunan wucin gadi.

Daga 2017 lokacin da hare-haren masu ikirarin jihadin ya tsananta zuwa yanzu alkaluman kungiyar ACLED mai sanya idanu kan rikicin na Mozambique ya ce mutane dubu 4 da 100 suka rasa rayukansu.

Zuwa yanzu akwai dakarun kasashen ketare akalla dubu 3 da 100 da ke aikin wanzar da zaman lafiya a yankin Cabo Delgado, dai dai lokacin da jami’an diflomasiyyar da ke shiga tsakani a rikicin ke cewa kungiyoyin yanzu haka sun rabu gida 3 tare da ci gaba da kaddamar da hare-hare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.