Isa ga babban shafi

Majalisar Uganda ta amince da dokar tsaurara hukunci ga masu auren jinsi

Bayan shafe sa’o’i ana tafka muhawara mai zafi, majalisar dokokin kasar Uganda ta kada kuri’ar amincewa da sabuwar dokar da ke tsaurara hukunci kan masu dabi’a ko goyon bayan auren jinsi guda a kasar. 

Majalisar dokokin Uganda yayin zaman amincewa da dokar da ta tsaurara hukunci ga masu auren jinsi.
Majalisar dokokin Uganda yayin zaman amincewa da dokar da ta tsaurara hukunci ga masu auren jinsi. REUTERS - ABUBAKER LUBOWA
Talla

Dama dai alakar auren jinsi guda haramtaciyya ce a Uganda, kafin matakin tsaurara hukuncin da majalisar kasar ta amince da shi  a baya bayan nan, ko da ya ke babu karin bayani  akan abinda sabuwar dokar ta kunsa, wadda a yanzu ake dakon sa hannun shugaba Yoweri Museveni akan ta kafin ta fara aiki. 

Daya daga cikin makusantan shugaban Museveni wanda kuma dan jam’iyar sa ne, Odoi-Oywelowo ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa AFP cewa a karkashin sabuwar dokar, ta tanadi daurin rai da rai ko kuma hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da aikata laifin.

Sai dai sa’oi kadan bayan amincewa da wannan doka, kungiyar ta kare hakkin bil’adama ta Amnesty International, ta bukaci shugaba Museveni da kada ya sanya hannu akan sabuwar dokar.

Amnesty ta ce amincewa da dakar da ta tsaurara hukunci ga masu auren jinsi ko goyon bayan su, zai kara rura wutar kyama da nuna banbanci  ga masu dabi’ar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.