Isa ga babban shafi

Adadin mutanen da suka mutu a guguwar Malawi ya doshi 400

Adadin wadanda suka mutu daga guguwar Freddy bayan ta afkawa Malawi da ke yankin kudancin Afirka ya kai 326, in ji shugaban kasar, wanda hakan ya kawo adadin wadanda suka mutu a yankin zuwa sama da 400 tun daga watan Fabrairu.

Iyalan wasu daga cikin wadanda suka mutu sakamakon guguwa dauke da ruwan sama mai karfin gaske a Malawi kenan.
Iyalan wasu daga cikin wadanda suka mutu sakamakon guguwa dauke da ruwan sama mai karfin gaske a Malawi kenan. REUTERS - ELDSON CHAGARA
Talla

Shugaba Lazarus Chakwera ya ce ya zuwa ranar Alhamis, adadin wadanda suka mutu sakamakon wannan bala'i ya karu daga 225 zuwa 326, adadin mutanen da suka rasa matsugunansu ya ninka fiye da 183,159, a yankin kudancin kasar.

Masu aikin ceto a Malawi da na ci gaba da lalubo gawarwakin da baraguzan gini suka danne.

Yayin da aka samu tsaikon ruwan sama a karon farko cikin kwanaki biyar, masu aikin ceto sun tono gawarwakin da ke makale a karkashin laka da baraguzan gidajen da guguwar ta tafi da su.

A wani aiki na hadin gwiwa da sojoji da mazauna yankin suka yi, sun gano gawarwakin mutane sama da goma a garin Manje mai tazarar kilomita 15 kudu da Blantyre babban birnin kasuwancin kasar, bayan da mazauna yankin suka ce sun hango kumfa da ke kunno kai a karkashin tarkacen laka.

Masu aikin ceto sun zakulo gawar wani dattijo da gini ya ruftawa a saman wani tsauni, inda suka nade shi a cikin wani bargo, kuma bayanai sun ce, said ai suka yi ‘yar tafiya zuwa wani wuri da motocin daukar marasa lafiya ke ajiye.

Hukumomin kasar sun ce adadin wadanda suka mutu ya zuwa yanzu ya kai 400, amma aadin zai iya karuwa, kasancewar an gano wasu wuraren da lamarin ya shafa a Manje.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.