Isa ga babban shafi

Mauritania na farautar 'yan ta'addan da suka tsere daga gidan yarinta

‘Yan ta’adda masu ikirarin jihadi 4 sun tsere daga wani gidan yari a Mauritania bayan sun afka wa jami’an tsaro, inda har suka kashe 2, kamar yadda ma’aikatar cikin gidan kasar ta sanar a jiya Litinin.

'Yan ta'addan sun tsere ne daga gidan yarin birnin Nouakchott.
'Yan ta'addan sun tsere ne daga gidan yarin birnin Nouakchott. Alexandra Pugachevsky/CC/Wikimedia
Talla

Ma’aikatar Cikin Gidan ta ce an tsaurara matakan tsaro a gidan yarin da ke babban birnin kasar, kuma tuni aka fara aikin farautar ‘yan ta’addan da suka arce.

Wata majiya ta ce,  Saleck Oud Cheikh, wanda tun a shekarar 2011 aka yanke wa hukuncin kisa bayan samun si da laifin yunkurin kisan shugaban kasar, Mohammed Ould Abdel Aziz na daya daga cikin fursunonin da suka tsere.

Wannan wani bakon al’amari ne a ksar Mauritania, wadda ba ta dandana radadin ayyukan ta’addancin da sauran takwarorinta na yakin Sahel ke fama da su ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.