Isa ga babban shafi
Cinikin bayi

'Har yanzu ana cinikin bayi a Mauritania'

Kungiyoyin fafutuka a Mauritania sun ce har yanzu ana cinikin bayi a kasar, duk da cewa an haramta hakan shekaru da dama da suka shude, yayin da gwamnati ke ci gaba da ikirarin kawar da wannan matsala.

Tun shekara ta 1808 aka haramta cinikin bayi a duniya,
Tun shekara ta 1808 aka haramta cinikin bayi a duniya, Henry P. Moore / Library of Congress / Wikimedia public domain
Talla

A shekarar 1981 aka haramta ciniki da bautar da bil’adama a Mauritania, inda dokar kasar ta ce duk wanda aka samu da aikata hakan, shakka babu ya aikata laifin cin zarafin bil’adama.

Wani taron kwanaki biyu, wanda kungiyoyin fafutuka daga kasashe biyar na yankin Sahel suka shirya sun koka matuka kan yadda ake bautar da bil’adama, bayan da hukumomi na duniya na ci gaba da wayar da kan gwamnatoci.

Kwamishinan Hukumar Kare Hakkin Dan Adam a Maurtania Cheikh Ahmedou Ould Sidi ya ce gwamnati na son yin aiki tare da kungiyoyin da ke aiki a cikin doka da kuma watsi da tsattsauran ra'ayi domin kawar da bauta.

Wakilan taron abin da suka yi fata shi ne a kawo karshen bautarwa da kuma cinikin gaba daya daga doron kasa, wanda suka ce shine ummul aba’isin aukuwar laifuka da dama.

Taron na kwanaki biyu ya kuma samu halartar wakilai daga Senegal da Gambia da kuma kasashen Turai da suka hada da Belgium da Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.