Isa ga babban shafi
Mali

Harin ta'addanci ya hallaka Sojin Mali 10 a iyakar kasar da Mauritania

Majiyar tsaro a Mali ta tabbatar da kisan Sojinta akalla 10 yayin wani farmakin tsakaddare da aka kai musu a sansaninsu da ke gab da iyakar kasar da Mauritania.

Wasu Sojin Mali da ke yaki da ta'addanci.
Wasu Sojin Mali da ke yaki da ta'addanci. MICHELE CATTANI / AFP
Talla

Wannan ne dai karo na 3 da makamancin farmakin ke haddasara asarar rayukan Sojin na Mali tun bayan da Soji suka yi juyin mulki a ranar 18 ga watan Agustan da ya gabata.

Wani rahoton ma’aikatar tsaron kasar da AFP ya samu, ya ce cikin wadanda harin ya rutsa da su har da wani babban jami’i guda baya ga manyan motocin yaki 4 da aka kone a farmakin gab da yankin Guire na kasar.

Mazauna garin na Guire sun shaidawa manema labarai cewa karar musayar bindiga tsakanin sojin da maharan ne ya tashe tsakaddaren jiya Alhamis wayewar yau Lahadi.

Wani mazaunin yankin na Guire ya shaidawa AFP cewa tun ranar litinin din da ta gabata suka fara ganin bakin fuska haye a babura sun shigo yankin sai dai babu cikakkiyar hujjar su suka kaddamar da farmakin.

Ko a ranar 27 ga watan Agustan da ya gabata sai da makamancin farmakin ya kashe sojin Mali 4 ya kuma jikkata wasu 12, ko da ya ke suma dakarun sun hallaka maharan 20 a wancan lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.