Isa ga babban shafi
Mali - Ta'addanci

'Yan bindiga sun sace 'yan China, Mauritania a Mali

‘Ya bindiga sun sace wasu ‘yan kasar China 3 da ‘yan Mauritania 2 a wani wajen gini dake kudu maso yammacin Mali, kamar yadda rundunar sojin kasar ta sanar.

Duk da ayyukan dakarun Barkhane a yankin Sahel, matsalar tsaro ta ci gaba da ta'azzara.
Duk da ayyukan dakarun Barkhane a yankin Sahel, matsalar tsaro ta ci gaba da ta'azzara. © Franck Alexandre/RFI
Talla

Maharani sun isa wajen ginin ne mai nisan kilomita 55 daga garin Kwala a jiya Asabar, suka kuma yi awon gaba da motocin akori-kura 5 da kuma mutanen da suka yi garkuwa da su.

‘Yan bindigar sun kuma lalata kayan aikin gine gine na wani kamfanin kasar China, a cewar wata sanarwa daga rundunar sojin kasar.

Kamfanin dillancin labarai na kasar Mauritania, Al-Akhbar ya ruwaito cewa ‘yan bindigar sun kai harin ne bisa babura, suka kuma yi kone konen kayan aikin kamfanin kafin daga bisani su yi awon gaba da mutanen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.