Isa ga babban shafi

Fiye da rabin mayakan jihadi na shiga kungiyoyin ta'addanci saboda kudi- UNDP

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa talauci da kuma yaudarar bayar da aiki mai tsoka ga jama’a shi ke rura wutar samun tarin matasan da ke shiga kungiyoyi masu ikirarin jihadi sabanin akida.

Fiye da rabin mayakan 'yan ta'adda sun shiga kungiyoyin da suke yiwa yaki ne saboda kudi.
Fiye da rabin mayakan 'yan ta'adda sun shiga kungiyoyin da suke yiwa yaki ne saboda kudi. ©REUTERS/Stringer
Talla

Sakamakon wani binciken kwakwaf da hukumar raya kasashe ta Majalisar dinkin duniya UNDP ta gudanar ya kawar da shakkun cewa mayakan da ke cikin irin wadannan kungiyoyi na aiwatar da hare-harensu ne bisa ikirari ko kuma fahimtar addini, sabanin haka binciken hukumar ya gano cewa suna cikin irin wadannan kungiyoyi ne kawai don samun kudaden tafiyar da rayuwarsu.

Hukumar UNDP ta bayyana cewa, galibin mayakan Boko Haram, al-Shabaab da Alqaeda da kuma kungiyar GSIM sun shiga kungiyar ne kawai ko dai saboda talauci ko kuma saboda an kwadaita musu samun aiki mai tsoka.

A cewar UNDP, a tattaunawar da ta yi da wasu mutane dubu 2 da 200 a kasashen Burkina Faso da Mali Kamaru da Nijar da Najeriya da kuma Chadi baya ga Sudan da Somalia da dukkaninsu ke fama da hare-haren irin wadannan kungiyoyi da ke ikirarin ko dai jihadi ko kuma kafa daular Islama, fiye da rabi sun nuna cewa suna shiga kungiyoyin ne saboda kudi sabanin akida.

UNDP ta ce kashi 1 bisa 3 na mayakan suna shiga kungiyoyin ne a radin kansu don samun kudade, yayinda kashi 22 ke shiga saboda tilasci ko kuma don samun damar zama da ahalinsu sai kuma kashi 17 da hukumar ke cewa su kadai cikin wadannan mayaka ke shiga kungiyoyin saboda dalili ko kuma aqida ta addini.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.