Isa ga babban shafi

Kotu ta daure mutane 8 da aka samu da hannu wajen harin ta'addanci a Nice

Wata Kotu a kasar Faransa ta yanke hukuncin dauri akan mutane 8 da aka samu da hannu wajen kai harin ta’addanci a Birnin Nice a shekarar 2018 wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane 86 da jikkata wasu sama da 450.

Zaman kotun da ta yi shari'ar harin ta'addancin Nice
Zaman kotun da ta yi shari'ar harin ta'addancin Nice © Benoit Peyrucq / AFP
Talla

Daga cikin mutanen 8 da aka samu da laifi, kotun ta daure guda 2 shekaru 18 – 18 saboda taimakawa Mohammed Lahouaiej-Bouhlel mai shekaru 31 kuma mazaunin kasar Tunisia shirya kai kazamin harin na mintina 4 da ya haifar da wannan aika aika kafin hallaka shi.

Alkalan kotun sun yanken hukuncin cewar Mohammed Ghraieb da Chokri Chafroud na da masaniya dangane da yadda wanda ya shirya kai harin ya rungumi tsatsauran ra’ayi da kuma aniyarsa ta kai hari saboda yadda bayanan sakonnin wayarsa suka nuna a tsakaninsu su 3 kafin kai harin.

An samu Ghraieb mai shekaru 47 da Lahouaiej-Bouhlel dake kasar Tunisia da Chafroud mai shekaru 43 da laifin taimakawa maharin hayar motar da yayi amfani da ita, yayin da suka ki amincewa da zargin.

Kotun ta samu Ramzi Arefa mai shekaru 28 da laifin taimakawa Lahouaiej-Bouhlel da bindigar da ya harbi yan sanda, saboda haka an daure shi shekaru 12 a gidan yari, duk da yake ba’a tuhume shi da mu’amala da yan ta’adda ba.

Sauran mutanen 5 da suka hada da dan kasar Tunisia guda da Yan kasar Albania 4 sun samu daurin tsakanin shekaru 2 zuwa 8 saboda samunsu da laifin safarar makamai da hada baki domin kai hari, amma kuma babu tuhumar dake da nasaba da ayyukan ta’addanci.

Wannan hari na Nice na daga cikin munanan hare haren ta’addancin da Faransa ta gani a cikin kasar ta, abinda ya sa kasar daukar matakai masu tsauri na yaki da ayyukan ta’addanci.

Akalla mutane 30,000 suka yi gangami a bakin ruwan Nice domin kallon wasan wuta lokacin bikin ranar yancin Bastille a ranar 14 ga watan Yuli lokacin da aka kai musu harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.