Isa ga babban shafi

An kama wasu tsoffin sojojin Faransa biyu a Bangui

A Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, 'yan sandan sama da kan iyaka sun kama wasu tsoffin sojojin Faransa biyu da ke aiki a ofishin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kasar (Minusca), a ranar Talata, 10 ga watan Janairu 2023, a lokacin da suka isa filin jirgin saman kasa da kasa na Bangui. Bayanin da Minusca ya tabbatar a cikin wata sanarwa ga manema labarai. 

Wasu daga cikin dakarun kasar Faransa a Bangui
Wasu daga cikin dakarun kasar Faransa a Bangui AFP - BARBARA DEBOUT
Talla

Sojojin biyu sun sauka a filin jirgin sama na Bangui da misalin karfe 4 na yamma agogon kasar a ranar Talata, 10 ga watan Janairun 2023, lokacin da jami’an ‘yan sandan na kan iyaka na Afirka ta Tsakiya suka kama su. A cewar wata majiyar diflomasiyya, nan take aka karbe fasfo dinsu, da katin shaida na Minusca da kwamfutocinsu, kafin a nuna su ga ‘yan jaridu a matsayin sojojin Faransa  wadanda ke kokarin  shiga kasar ba tare da kowa ba bisa, da nufin tada zaune tsaye a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

An ce an kama sojojin biyu ne kawai saboda lambar sheidar su ta kasance har zuwa Disamba 2023 don haka ba a daidaita su da biza nasu wanda zai kare a watan Maris na wannan shekara.

Wannan majiyar a ƙarshe ta tabbatar da cewa ba da daɗewa ba za a saki mutanen biyu, saboda 'yan sanda sun samu bayanan da suke so.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.