Isa ga babban shafi

Karim Khan na kotun ICC ya ziyarci yankunan da aka gano kaburbura a Libya

Babban mai shigar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta Duniya ICC Karim Khan ya gana da iyalan wadanda ake zargin kungiyoyi masu rike da makamai sun yiwa kisan gilla a Libya, a wata ziyarar aiki da ya faro a farkon makon nan a kasar mai fama da rikicin fiye da shekaru 10.

Babban mai shigar da kara na kotun ICC Karim Khan.
Babban mai shigar da kara na kotun ICC Karim Khan. AFP - ABDELMONIM MADIBU
Talla

A ziyarar da ya faro tun a litinin din farkon makon nan ne Karim Khan ya gana da iyalan wadanda wannan kisa ya rutsa da ahalinsu baya ga kai ziyarar gani da ido yankuna da aka gano manyan kaburburan da ke dauke da tarin mutanen da aka yiwa kisan gillar a gab kauyen Tarhuna da ke kudu maso gabashin birnin Tripoli baya ga sassan da ka rika gano gawarwaki cikin gonakin jama’a a 2020.

Yayin ganawarsa da Iyalan, Khan ya jaddada musu kudirinsa na ganin an bi musu hakki ta hanyar hukunta wadanda ke da hannu, batun da tuni ICC ta wallafa a shafinta na Twitter.

Karim Khan wanda ya isa Libya tun a asabar din da ta gabata, shi ne babban mai shigar da kara na farko daga ICC da ke ziyartar kasar wadda ta yi fama da rikicin fiye da shekaru 10.

A ziyarar ta Mr Khan ya kuma gana da manyan mukarraban gwamnatin Libya da suka kunshi shugaban Majalisar zartaswa Mohamed el-Manfi da kuma ministar shari’a Halima Ibrahim baya ga babban mai shigar da kara bangaren Soji.

ICC ta bayyana cewa kowanne lokaci a yau ne Khan zai yiwa kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya karin bayani kan halin da ake ciki a kasar ta Libya.

Fiye da gawarwakin fararen hula 270 aka gano cikin kabari guda a gab da kauyen na Tarhouna yayin wani binciken kungiyoyin kasa da kasa.

Haka zalika ko a watan Yunin 2020 sai da aka gano manya-manyan kaburbura makare da gawarwakin fararen hula kwanaki kalilan bayan janyewar dakarun da ke biyayya ga Khalifa Haftar daga yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.