Kotun ICC ta yi bikin cika shekaru 20 da kafuwa
Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ICC, ta yi bikin cika shekaru 20 da kafuwa a ranar Juma’a, inda yakin Ukraine ya sanya hankula karkata ga kotun don ganin matakan da za ta dauka dangane da zarge-zargen take hakkin dan adam da sauran laifukan yakin da ake zargin an aikata.
Wallafawa ranar:
Wasu dai na kallon har yanzu kwalliya bata biya kudin sabulu ba dangane da manufar kotun da ta kafu tun ranar 1 ga Yuli, na shekara ta 2002, la’akari da cewar manyan shara’o’i biyar ta samu nasarar kammalawa tare da yanke hukunci a cikinsu.
Sai dai har yanzu kotun ta ICC ce madafa ta karshe ga masu neman hakkinsu kan laifukan da suka hada da cin zarafin dan adam, kisan kiyashi, da kuma laifukan yaki a duk lokacin da kasashe mambobin ta suka gagara ko kuma suka ki gabatar da kara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu