Isa ga babban shafi

ICC da EU za su yi binciken hadin-guiwa kan yakin Ukraine

Hukumar shari’ar kungiyar kasashen Turai EU Eurojust, ta ce babban mai shigar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, zai shiga tawagar jami’anta, domin gudanar da bincike kan zarge-zargen aikata laifukan yaki a Ukraine.

Hare-haren Rasha sun lalata sun tilasta wa miliyoyin mutane kaurace wa gidajensu
Hare-haren Rasha sun lalata sun tilasta wa miliyoyin mutane kaurace wa gidajensu REUTERS - ALEXANDER ERMOCHENKO
Talla

Wannan dai shi ne karo na farko da kotun ICC, wadda aka kafa a shekarar 2002 mai hedikwata a birnin Hague za ta shiga binciken hadin gwiwa da wasu kasashe kan laifukan yakin da aka aikata a wata kasa.

Tuni dai babban mai shigar da kara na kotun ta ICC Karim Khan ya rattaba hannu kan kulla yarjejeniya da masu gabatar da kara na kasashen Lithuania da Poland da kuma Ukraine, domin shiga cikin tawagarsu ta hadin guiwa da za ta gudanar da bincike kan laifukan yaki da cin zarafin bil adama da aka aikata tun bayan yakin da Rasha ta kaddamar kan Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairu.

Kusan makwanni biyu da suka gabata, Karim Khan ya ziyarci garin Bucha, inda aka gano wani makeken kabari dauke da gawarwakin fararen hula kusan 300, baya ga wadanda aka yasar kan tituna, ta’asar da Ukraine ta ce ko shakka babu sojojin Rasha ne suka aikata a lokacin da suka mamaye garin tsawon makwanni.

Rasha dai na cigaba da musanta cewar sojojinta ne suka kashe daruruwan fararen hular, zalika shugaba Vladimir Putin ya yi watsi da rahotannin cewa dakarunsa na kaiwa fararen hula hari da gangan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.