Isa ga babban shafi

Kotun ICC ta yi watsi da bukatar Myanmar kan shari'ar kisan kiyashin Rohingya

Babban kotun Majalisar Dinkin Duniya ta yanke hukuncin ci gaba da gudanar muhimmin shari'a da ke zargin gwamnatin Myanmar da laifin kisan kare dangi a kan tsirarun musulmin kabilar Rohingya.

Wasu daga cikin 'yan kabilar Rohingya dake gudun hijira a Bangladesh.
Wasu daga cikin 'yan kabilar Rohingya dake gudun hijira a Bangladesh. REUTERS/Rafiqur Rahman
Talla

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da ke birnin Hague ta yi watsi da duk wani matakin da Myanmar ta dauka kan karar da kasar Gambiya da ke yammacin Afirka ta shigar a shekarar 2019.

Matakin dai ya share fagen ci gaba da sauraren shari'a a kotun kan zargin kisan gillar da aka yi wa 'yan kabilar Rohingya a shekarar 2017 da mabiya addinin Buda mafiya rinjaye a Myanmar suka yi.

Dubban ‘yan kabilar Rohingya ne suka tsere daga kudu maso gabashin Asiya yayin farmakin shekaru biyar da suka gabata, inda suka bayyana munanan rahotannin kisan kai, fyade.

Bangladesh

Kimanin 'yan Rohingya 850,000 ne ke cikin mawuyacin hali a sansanoni a makwabciyarta Bangladesh yayin da wasu 'yan Rohingya 600,000 suka rage a jihar Rakhine da ke kudu maso yammacin Myanmar.

Ministan shari'a na Gambia Dawda Jallow ya shaidawa manema labarai a wajen kotun cewa "ya ji dadin yadda kotun ta yi adalci".

'Yan gwagwarmayar Rohingya da dama sun yi zanga-zanga a wajen kotun yayin da ake sanar da hukuncin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.