Isa ga babban shafi
BANGLADESH - ROHINGA

An kasashe 'yan gudun hijirar Rohingya 7 a sansanin Bangladesh

Wasu 'Yan bindiga sun bude wuta a sansanin 'Yan gudun hijirar Yan kabilar Rohingya dake Bangladesh, inda suka kasha mutane 7 da kuma jikkata wasu akalla 20.

Sansanin 'yan gudun hijirar Rohingya dake kasar Bangladesh 24/10/21.
Sansanin 'yan gudun hijirar Rohingya dake kasar Bangladesh 24/10/21. AP - Shafiqur Rahman
Talla

Babban jami’in 'Yan Sandan yabkin yace Yan bindigar sun bude wuta ne akan mai uwa da wabi, yayin da suka kuma daba wuka a sansanin Balukhali dake Yankin Coz Bazar, kusa da iyakar Myanmar.

'Yan bindiga sun kashe mutane bakwai tare da raunata akalla 20 ranar Juma'a a sansanin' yan gudun hijirar Rohingya da ke Bangladesh, 'yan sanda da likitoci sun ce, harin da ke kara tayar da hankula na zuwa ne bayan harbe wani fitaccen jagoran al'umma a kwanan nan.

Sansanin 'yan gudun hijirar Rohingya dake kasar Bangladesh 24/10/21.
Sansanin 'yan gudun hijirar Rohingya dake kasar Bangladesh 24/10/21. - AFP

Maharan sun harbe mutanen da ke halartar makarantar Islamiyya a sansanin tare da caka musu wuka, in ji wani shugaban ‘yan sandan yankin.

Mutane hudu sun mutu nan take. Wasu mutane uku sun mutu a asibiti a ɗaya daga cikin sansanin 'yan gudun hijira na Balukhali, wani ɓangare na matsugunin dake ke ɗauke da mutane 900,000.

'Yan sanda ba su bayyana adadin mutanen da suka jikkata ba amma wani likita dake aiki da Doctors Without Borders (MSF) wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce kimanin mutane 20 sun samu munanan raunuka.

Sansanin 'yan gudun hijirar Rohingya dake kasar Bangladesh.
Sansanin 'yan gudun hijirar Rohingya dake kasar Bangladesh. Munir Uz zaman AFP

Jami'in 'yan sanda Kamran Hossain ya ce "Miyagun' yan Rohingya" sun shiga cikin darul Ulum Nadwatul Ulama al Islamia madrassa kafin wayewar gari inda suka harbe mutane a ciki".

Nan take jami’an tsaro suka rufe sansanin, wanda ke dauke da mutane sama da 27,000.

Mazauna sansanin sun yada hotuna a kafafen sada zumunta na gawarwaki.

Wasu daga cikin miliyoyin 'yan kabilar Rohingya da ke zaune a sansanin 'yan gudun hijira na Kutupalong da ke Ukhia, a kasar Bangladesh.
Wasu daga cikin miliyoyin 'yan kabilar Rohingya da ke zaune a sansanin 'yan gudun hijira na Kutupalong da ke Ukhia, a kasar Bangladesh. Tanbir Miraj AFP

Shugaban 'yan sandan yankin Shihab Kaisar Khan ya shaida wa manema labarai cewa, "sun cafke maharin daya bayan faruwar lamarin."

Ya kara da cewa an samu mutumin da bindiga, harsasai shida da wuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.