Isa ga babban shafi

Gwamnatin Sojin Guinea za ta gurfanar da Conde don fuskantar hukunci kan rashawa

Sojojin da ke mulki a Guinea sun bada umarnin gurfanar da tsohon shugaban kasar Alpha Conde tare da wasu jami’an gwamnatinsa sama da 180 bisa zargin su da cin hanci da rashawa.

Dakarun gwamnatin Sojin Burkina Faso.
Dakarun gwamnatin Sojin Burkina Faso. © AP - Sunday Alamba
Talla

Sojojin da suka yi wa Conde juyin mulki a ranar 5 ga watan Satumban bara, sun ce suna bayar da muhimmanci ga duk wani batu na yaki da cin hanci da rashawa, matsalar da ake kallo a matsayin annoba a kasashen yammacin Afrika.

Daga cikin mutanen da sojojin suka bukaci masu shigar da kara na gwamnati su tuhuma, har da tsohon firamanistan kasar, Ibrahima Kassory Fofana da tsoffin ministocin tsaro da na tattalin arziki da wasu tarin tsoffin masu bada shawara ga shugaban kasa da suka yi aiki a karkashin mulkin Conde.

Sojojin sun kuma bada umarnin farautar sauran mutanen da ake zargi da yin wadaka da dukiyar al’ummar kasar kamar yadda wata sanarwa da suka fitar ta nuna.

Sanarwar na kunshe da sunayen mutane 188, ko da ya ke wasu sunayen an ambace su fiye da sau daya a cikin sanarwar, yayin da aka dakatar da jerin asusunsu na bankuna.

Guinea na ci gaba da kasancewa karkashin mulkin soji tun bayan juyin mulkin da suka yi wa Conde wanda ya shafe sama da shekaru 10 kan karagar mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.