WHO za ta fara gwajin rigakafin cutar Ebola a Uganda
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce nan da makwanni za a fara gudanar da gwaje-gwaje kan allurar rigakafin cutar Ebola domin dakile yaduwar cutar wadda ta barke a kasar Uganda.
Wallafawa ranar:
A watan da ya gabata ne Kampala ta sanar da samun mace-mace na farko a Uganda daga cutar mai saurin yaduwa, karon farko tun shekarar 2019, inda wata sanarwa da hukumar ta WHO ta fitar ta ce gwaji ya tabbatar da samun cutar a jikin mutum 54 da kuma mutuwar mutane 19.
Ministar lafiya ta kasar Uganda Jane Ruth Aceng ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa an samu mutuwar mutum guda a birnin Kampala bayan ya tsere daga tsakiyar gundumar Mubende inda aka fara samun bullar cutar.
A halin yanzu babu wani maganin rigakafin cutar Ebola nau’in Sudan da ke yaduwa a gabashin Afirka.
An dai fara samun bullar cutar ne ranar 20 ga watan Satumba, a yankuna biyar da suka hada da Mubende, a cewar WHO.
Wani bincike da hukumar lafiya ta duniya WHO ta gudanar ya gano cutar Ebola nau’in Sudan na barazanar yaduwa zuwa makwabtan kasashe saboda zirga-zirgar kan iyaka tsakanin Uganda da wasu kasashe.
Annobar mafi muni a yammacin Afirka ta auku ne tsakanin shekarar 2013 zuwa 2016 inda ta kashe mutane fiye da 11,300.
Uganda ta fuskanci bullar cutar Ebola da dama, na baya-bayan nan shine na shekarar 2019 inda akalla mutane biyar suka mutu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu