Isa ga babban shafi

Karin mutane 19 sun harbu da Ebola a Uganda bayan da cutar ta kashe mutane 4

Ma’aikatar lafiyar Uganda ta sanar da mutuwar wasu karin 3 sanadiyyar cutar Ebola wanda ke mayar da adadin wadanda cutar ta kashe zuwa mutum 4 daga bullarta a farkon makon nan zuwa yanzu.

Ma'aikatar lafiyar ta sanar da samun karin mutanen da suka yi mu'amala da wadanda suka harbu da cutar.
Ma'aikatar lafiyar ta sanar da samun karin mutanen da suka yi mu'amala da wadanda suka harbu da cutar. Baz Ratner/Reuters
Talla

Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta ce zuwa yanzu alkaluman wadanda aka tabbatar sun harbu da cutar ya kai 11 bayan samun karin mutum 4 a jiya juma’a, said ai ma’aikatar ba ta bayar da karin bayani kan ko jumullar mutanen 11 ta kunshi har da 4 da suka mutu ko akasin haka.

Ma’aikatar lafiyar ta Uganda ta kuma ce akwai karin mutane 19 da suka yi mu’amala da masu cutar ta Ebola wadanda suma ake tsammanin sun harbu da cutar mai hadari. 

Sanarwar ta ce tawagar kwararru da ke aikin yaki da cutar na ci gaba da laluben mutanen da suka yi mu’amala da wadanda aka tabbatar sun harbu da cutar don basu kulawar da ta kamata.

Wannan ne karon farko da Uganda ke ganin bullar cutar ta Ebola tun bayan kawar da ita a shekarar 2019 wanda ake alakantawa da ganin cutar a makwabciyar kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.