Isa ga babban shafi

Sabon fada ya barke a Libya tsakanin bangarorin da ke yakar juna

Sabon fada ya barke tsakanin bangarorin da ke rikici da juna a birnin Tripoli na Libya yau asabar inda bayanai ke cewa magoya bayan Haitham al-Tajouri sun farmaki mayakan Abdel-Ghamo al-Kikli.

Sintirin jami'an tsaro a tsakar birnin Tripoli.
Sintirin jami'an tsaro a tsakar birnin Tripoli. © Reuters
Talla

Wasu ganau sun ce magoya bayan al-Tajaouri jagoran dakarun juyin juya halin birnin Tripoli ne suka farwa mayakan al-Kikli da ke rike da makamai tare da nsara kansu.

A cewar rahotanni dakarun na Haitham sun kame mayakan na al-Kikkli 3 da ake alakantawa da hare-hare kan fararen hula da dakarun gwamnati baya ga kwace tarin motocinsu da kuma karbe iko da shalkwatarsu da ke birnin na Tripoli.

Libya ta fada cikin mummunan yakin basasa ne tun bayan hambararwa da kuma kisan jagoranta Mu’ammar Gaddafi a shekarar 2011, ta yadda aka samu rarrabuwar kai da kuma bayyanar kungiyoyin masu rike da makamai da ke yakar juna.

Har zuwa yanzu dai bangaren gabashin kasar na karkashin ikon Kwamandan Sojin Libyan ne Khalifa Haftar yayin da Majalisar Dinkin Duniya ke goyon bayan gwamnatin yammacin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.