Libya na tafka hasarar dala miliyan 60 a kowace rana - Minista
Ministan man Libya Muhammed Aoun, ya ce kasarar na tafka hasarar dala miliyan 60 a kowacce rana sakamakon rufe cibiyoyin hakar danyen man kasar, a daidai lokacin da farashin gangarsa ta yi tashin gwauron zabi a duniya.
Wallafawa ranar:
Man fetur dai shi ne ginshikin tattalin arzikin kasar ta Libya da ke kokarin murmurewa daga rikicin tsawon shekaru 10, biyo bayan kifar da gwamnatin shugaba Moamer Kadhafi a wani boren da kungiyar tsaro ta NATO ta marawa baya a shekara ta 2011.
Sai dai tun a tsakiyar watan Afrilu rikicin siyasar Libya na baya bayan nan, ya gurgunta ayyukan manyan tashoshin jiragen ruwa guda biyu da kuma rijiyoyin mai da dama a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu