Isa ga babban shafi
Libya

Libya za ta dawo da fitar da Fetur

Jami'an Tsaron da ke adawa da gwamnatin hadin kan kasar Libya sun mika ragamar tafiyar da tashoshin fitar da man fetur din kasar guda hudu ga kamfanin man kasar bayan mamaye su da suka yi.

Tashoshin fitar da man fetur a Libya
Tashoshin fitar da man fetur a Libya STRINGER / AFP
Talla

Kanar Ahmad Mesmari, mai Magana da yawun kamfanin ya sanar da cewar daga jiya laraba sun mika tashohin na Zuwaytina da Brega da Ras Lanuf da kuma Al Sidra ga kamfanin man kasar dan ci gaba da tafiyar da su.

Firaministan riko Fayez al-Sarraj ya tattauna da shugaban 'yan tawayen Fil Mashal Khalifa Haftar dan samun wanann nasara.

Rikicin kasar Libya dai ya durkusar da duk wata hanyar samun Kudin shiga a kasar inda ake gani soma fitar da Man a yanzu zai cike wani gibin tattalin arzikin kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.