An kwashe sinadaran hada makami mai guba daga Libya
Hukumomin kasar Libya sun ce an kwashe kaso na karshe na sinadarin hada makami mai guba daga kasar a karkahsin shirin Majalisar Dinkin Duniya.
Wallafawa ranar:
Wani jami’in tsaron kasar ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar, cikin sinadarin da aka kwashe akwai tankuna 23 na siandarin da aka aika da shi kasar Jamus a jirgin ruwan Denmark.
Mataimakin Firaministan kasar Mussa el-Koni ya tabbatar da kwashe sinadaran.
Batun yunkurin mallakar makami mai guba yana daya daga cikin dalilan da suka kara tsamin dangantaka tsakanin tsohon shugaban Libiya marigayi Mu'ammar Gaddafi a waccan lokaci da kuma turawan yamma.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu